Ka’idar Kare Sirri

Kamfanin Mota-Engil Nigeria Limited, (daga yanzu za’a dinga kiran sa “Mota-Engil Nigeria”), wanda yake dukkan kokarinsa na ganin ya samar da tsaro ko kariyar Bayanan Sirri na Mutum.

Saboda haka, Mota-Engil Nigeria ta tsara wannan Manufar Kare Sirrin domin bayyana yadda take tattarawa da sarrafa bayanan sirri na mutane, bisa tanadin Dokar Kare Bayanai ta Najeriya ta shekarar 2023 (wanda daga yanzu za’a kira NDPA).

Sarrafa bayanan sirri da aka bayyana a cikin wannan Manufar ya shafi bayanan sirri na dukkan mutane dake mu’amala da Mota-Engil Nigeria ta kowacce  hanya.

Wannan takarda tana bayyana yanayi da hanyoyin da Mota-Engil Nigeria ke bi wajen sarrafa bayanan sirri na ‘yan kasa, waɗanda daga yanzu za’a kira ‘Masu Bayanai’ (Data Subjects). Mota-Engil Nigeria tana mutunta haƙƙin sirri na Masu Bayanai, kuma tana bayyana muku cewa tana bin dukkan dokoki da ƙa’idojin da suka dace game da kare sirri da kariyar bayanan sirri. Haka kuma, tana ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da sirri, kariya da amincin bayanan sirri da Masu Bayanai suka bayar.

Domin samun cikakkiyar fahimta game da yadda ake sarrafa bayanan sirri, manufofin sarrafa su, da haƙƙoƙin Masu Bayanai, muna ba da shawarar a dinga nazarin wannan Manufar Kare Sirri akai-akai.

Wake da alhakin sarrafa bayanan sirrinka?

Mota-Engil Nigeria ita ce mai kula da sarrafa bayanai (Data Controller) bisa tanade-tanaden Dokar Kare Bayanai ta Najeriya (NDPA), kuma ana iya tuntubar ta, ta lambar waya +234 9010400020 ko ta hanyar ziyartar ofishinta dake 19A, Adeola Odeku Street, Victoria Island, Lagos, Nigeria.

Wadanne irin bayanan sirri ne muke tattarawa?

Bayanan sirri da muke tattarawa sun danganta da yanayin hulɗar da ake yi da Mota-Engil Nigeria, a cikin tsarin ayyukanta na kasuwanci da kuma bisa tanade-tanaden dokokin da suka rataya a kanta.

Mota-Engil Nigeria tana tattarawa da sarrafa bayanan sirri da Mai Bayani (Data Subject) ya bayar da son ransa ta hanyoyin hulɗa daban-daban da aka kafa, ko dai kai tsaye, ta yanar gizon kamfanin, ta waya, wasiƙa ko ta Sakon karta kwana.

Duk wani bayani da Mai Bayanai ya bayar za’a yi amfani da shi ne kawai domin manufar da aka bayyana, tare da cikakken bin dokoki da ƙa’idojin kare bayanai.

Menene dalilan tattara bayanan sirrinka, kuma mene ne tushen doka da ake amfani da shi wajen sarrafa su?

Mota-Engil Nigeria tana tabbatar da cewa za’a sarrafa bayanan sirrika ne kawai a cikin iyakar manufar da aka tattara su dominta, ko kuma domin wasu manufofi da suka dace da ainihin dalilin da ya sa aka tattara su. Haka kuma, za mu sarrafa bayanan sirrika domin duk wasu manufofi da dokoki suka tanada.

Ayyukan taimakon masu hulda damu.

Mota-Engil Nigeria tana amfani da bayanan sirri na abokan huldarta domin taimako da kuma amsa kowace tambaya ko buƙata daga abokan hulda. Wannan yawanci yana buƙatar amfani da bayanan tuntuɓa na sirri da kuma bayanai game da tambayar abokin hulda (misali: buƙatar bayani, odar ayyuka, ƙorafe-ƙorafe game da kaya ko sabis, tambayoyi na gaba ɗaya, shawarwari, yabo, da sauransu). A irin waɗannan yanayi, dole ne a sarrafa bayananka domin cika kwangilar da aka sanya hannu tsakaninka da Mota-Engil Nigeria, ko kuma domin aiwatar da duk wani mataki da ake yi kafin kulla kwangila dangane da buƙatarka. Idan ba ka bayar da bayananka ba, ba za mu iya samar da bukatar da ake nema ko aka kulla ba. Bayananka za’a adana su domin wannan manufa tsawon lokacin da kwangilar ke aiki, sannan a ƙara shekaru 10 bayan ta ƙare. Bayanai na masu yiwuwar zama abokan hulda za’a adana su na tsawon shekaru biyu. Haka kuma, bayanan sirri na abokan hulda na iya kasancewa ana sarrafa su daga Mota-Engil Nigeria domin gudanar da shari’o’i (litigation). Dalilin doka yana dogara ne kan halaccen buƙata (legitimate interest) na Mota-Engil Nigeria, kuma za’a adana bayanan ne tsawon lokacin da ya dace domin amfani wajen kare ko aiwatar da haƙƙoƙin da suka shafi hakan.

Sadarwar Tallata Kasuwanci

Mota-Engil Nigeria, tare da yardar abokan hulda (idan ya zama dole), za ta yi amfani da bayanan sirri na abokan hulda domin ba su bayanai game da sabbin kaya, kayayyaki ko ayyuka (misali: sadarwar tallata kayayyaki ko kamfen da kuma tallace-tallace na musamman). Ana iya yin wannan ta hanyar imel, tallace-tallace, saƙonnin SMS, kiran waya, da wasiƙu ta gidan waya, gwargwadon yadda doka ta amince. Wasu daga cikin kamfen da tallace-tallacen Mota-Engil Nigeria ana gudanar da su ne a shafukan yanar gizo na wasu kamfanoni da/ko kafafen sada zumunta. Wannan amfani da bayanan sirri na abokan hulda ya dogara ne da yardarsu, wanda ke nufin za su iya janye yardarsu a duk lokacin da suka ga dama. Za’a adana bayanan abokin hulda domin wannan manufa har zuwa lokacin da mai bayanan ya yi amfani da haƙƙinsa na janye yardarsa.

kula da Ƙorafe-ƙorafe da Saƙonnin da Aka Karɓa

A mu’amalarsu da Mota-Engil Nigeria, abokan hulɗa na iya aiko mana da shawarwari ko ƙorafe-ƙorafe game da ayyukan da Kamfanin ke bayarwa. A irin waɗannan yanayi, za’a tattara bayanansu domin nazari da warware matsalar da ke tattare da buƙatar ko ƙorafin da aka gabatar, kuma za’a sarrafa bayanan ne bisa ga halaccen buƙatar Mota-Engil Nigeria.

Taruka

A taruka da Mota-Engil Nigeria ke shirya, dole ne a sarrafa bayanan sirri domin yin rajista da kuma ba da damar halartar taron. Haka kuma, ana iya tattara hotuna tare da samun yardar mai bayanan da ta dace. A wasu yanayi na musamman da ba zai yiwu a samu wannan yarda tun da wuri ba, Mota-Engil Nigeria na iya sarrafa bayanan bisa ga halaccin buƙatunta. Duk da haka, ana kiyaye haƙƙin mai bayanan na janye yardarsa ko kuma ƙin amincewa da sarrafa bayanansa. Za’a adana bayanan abokin hulɗa domin wannan manufa har zuwa lokacin da mai bayanan ya yi amfani da haƙƙinsa na janye yardarsa ko kuma ya ƙi amincewa da sarrafa bayanansa.

kula da Bayanai na Masu Samar da Kaya da Ayyuka

Dole ne a sarrafa bayanan masu samar da kaya da ayyuka domin cika kwangilar da aka kulla tsakanin mai samar da kaya ko ayyuka da Mota-Engil Nigeria, ko kuma domin aiwatar da duk wani mataki da ake yi kafin kulla kwangila. Idan ba a bayar da bayanan ba, ba za mu iya cika ayyukan da aka kulla a ƙarƙashin kwangilar ba. Za’a adana bayanan domin wannan manufa tsawon lokacin da kwangilar ke aiki, sannan a ƙara shekaru 10 bayan ƙarewar kwangilar. Bayanai na masu yiwuwar zama abokan hulɗa za’a adana su na tsawon shekaru biyu. Haka kuma, Mota-Engil Nigeria na iya sarrafa bayanan sirri na masu samar da kaya da ayyuka domin gudanar da shari’o’i. Dalilin doka yana dogara ne kan halaccen buƙatar Mota-Engil Nigeria, kuma za’a adana bayanan ne na tsawon lokacin da ake buƙata domin kare ko aiwatar da haƙƙoƙin da suka shafi hakan.

Bugu da ƙari, bayanan masu samar da kaya da ayyuka na Mota-Engil Nigeria, musamman ma’aikatansu, na iya kasancewa ana raba su ga abokan hulɗar Mota-Engil Nigeria domin cika wajibai na doka ko waɗanda suka samo asali daga yarjejeniyoyin kwangila.

Daukar Ma’aikata

Mota-Engil Nigeria, yayin da ta buɗe gurbin aiki ko kuma bayan karɓar takardar neman aiki, za ta sarrafa bayanan masu neman aiki domin tantance da ɗaukar ma’aikata, idan hakan ya zama dole domin aiwatar da matakan da ake bi kafin kulla kwangilar aiki. Za’a adana bayanan sirri da aka tattara na tsawon shekaru biyu (2) a mafi yawan lokuta idan mai neman aikin bai samu gurbin aikin ba. Bayan samun yardar mai bayanan, za mu iya adana bayanansa na tsawon lokaci fiye da shekaru biyu (2) idan mai bayanan yana son a yi la’akari da shi domin duk wata damar aiki a nan gaba wadda ta dace da ƙwarewarsa, cancantarsa ko bayanan da ya gabatar.

Na’urar tsaro ta bidiyo (Video Surveillance System)

Mota-Engil Nigeria tana amfani da na’urar tsaro ta bidiyo a harabobinta domin tabbatar da tsaron mutane da dukiyoyi. Bisa ga halaccin buƙatar Mota-Engil Nigeria, za mu tattara hotunan duk mutanen da suka shiga harabobinmu, amma ba tare da ɗaukar sauti ba. Ana iya miƙa waɗannan bayanai ga ’yan sanda masu binciken laifuka ko hukumomin shari’a idan suka nema bisa ƙa’ida. Za’a adana hotunan da aka tattara na tsawon kwanaki talatin (30) daga lokacin da aka ɗauke su (sai dai idan wata doka ta tanadi wani lokaci daban).

Nadar Kiran Waya

Lokacin da aka tuntuɓi Mota-Engil Nigeria ta waya, kuma a cikin tsarin gudanar da harkokin kasuwancinta, za mu iya nadar kiran wayar bayan mun sanar da mai kiran hakan tare da samun yardarsa. Ana yin hakan ne domin gudanar da hulɗar da ke gabanin kulla kwangila, inganta ayyukanmu da kuma tabbatar da inganci, bisa ga halaccin buƙatar Mota-Engil Nigeria.

Za’a adana waɗannan nadin kiran waya na tsawon lokacin da Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya (Nigeria Data Protection Commission – NDPC) ta tanada domin wannan aiki, tare da bin tanade-tanaden Dokar Kare Bayanai ta Najeriya (NDPA).

Tsawon Wane Lokaci Kake aje bayanin sirrinka?

Har tsawon wane lokaci muke adana bayanan sirrika?

Za’a adana bayanan sirri da aka tattara kuma aka sarrafa bisa ga manufar da aka tattara su domin ta, tare da bin wa’adin adanawa da dokoki suka tanada.

Idan babu wani takamaiman wa’adin doka da ya tanadi tsawon lokacin adanawa da riƙe bayanan sirri, za’a adana bayanan ne na tsawon lokacin da ya dace kuma ya zama dole, la’akari da manufar da aka tattara su domin ta. Hakan zai ci gaba ne sai dai idan mai bayanan, a cikin wa’adin da doka ta tanada, ya yi amfani da haƙƙinsa na ƙin amincewa da sarrafa bayanansa, ko ya nemi a goge su, ko kuma ya janye yardarsa.

Da zarar an kai iyakar wa’adin adanawa, za’a mayar da bayanan sirrin zuwa bayanan da ba za’a iya danganta su da wani mutum ba ta hanyar tsarin da ba za’a iya juyawa baya ba (irin waɗannan bayanan za’a iya ci gaba da adana su), ko kuma a lalata su cikin aminci.

Dangane da manufofin talla da sadarwa, za’a adana bayanan sirri bayan an samu yardarka, kuma za su ci gaba da kasancewa a ajiye muddin ba ka janye wannan yardar ba.

Mene Ne Haƙƙoƙin Masu Bayanai na Sirri?

Bisa ga dokokin da suka dace, masu bayanan sirri suna da haƙƙoƙi kamar haka:

  • Haƙƙin Samun Bayanai (Right of Access): Haƙƙin samun tabbaci kan ko ana sarrafa bayanan sirri ko a’a, kuma idan ana sarrafa su, a ba da damar samun waɗannan bayanan. A irin wannan yanayi, Mota-Engil Nigeria tana da haƙƙin neman a biya kuɗin da ya dace domin rufe kuɗaɗen gudanarwa da suka shafi samar da bayanan.
  • Haƙƙin Gyaran Bayanai (Right to Rectification): Haƙƙin neman a gyara bayanan sirri da ba daidai ba, da kuma neman a cika bayanan da ba su kammala ba.
  •  Haƙƙin Goge Bayanai (Right to Erasure): Haƙƙin neman a goge bayanan sirri, sai dai a lokutan da akwai dalilai na doka ko wasu hujjoji da ke ba da damar ci gaba da adana su.
  • Haƙƙin Taƙaita Sarrafa Bayanai (Right to Restrict the Processing): Haƙƙin neman a taƙaita sarrafa wasu rukunai na bayanai ko kuma sarrafa bayanai domin wasu takamaiman manufofi.
  • Haƙƙin Canja Wurin Bayanai (Right of Portability): Haƙƙin karɓar bayanan sirri da suka shafe shi ko ita a cikin tsarin da aka tsara, wanda aka saba amfani da shi kuma na’ura za ta iya karantawa, tare da haƙƙin miƙa waɗannan bayanai ga wani mai kula da bayanai.
  • Haƙƙin Ƙin Amincewa (Right to Object): Haƙƙin yin ƙin amincewa, a kowane lokaci, da sarrafa bayanan sirri, kamar sarrafa bayanan sirri domin talla kai tsaye.
  • Haƙƙin Kada a Yanke Masa Hukunci Ta Hanyar Tsarin Na’ura Kawai, Ciki Har da Tsara Bayanan Mutum (Profiling) (Right not to be Subject to Individual Automated Decisions, including Profiling): Haƙƙin kada a yanke wani hukunci da ya shafe shi ko ita bisa sarrafa bayanai ta hanyar na’ura kawai, ciki har da tsarin tantancewa ko tsara bayanan mutum (profiling), idan irin wannan hukunci zai haifar da sakamako na doka ko wani tasiri mai muhimmanci makamancin haka ga mai bayanan.

Domin amfani da waɗannan haƙƙoƙi, masu bayanai za su iya tuntuɓar mu ta hanyoyin sadarwa da aka bayyana a sashen “Bayanan Tuntuɓar Mai Kula da Bayanai” da ke ƙasa.

Masu bayanai kuma suna da haƙƙin janye yardarsu a duk lokacin da suka ga dama idan sun taɓa bayar da ita, ta amfani da hanyoyin tuntuɓar da aka ambata a sama. Duk da haka, janye yarda ba zai shafi ko soke sahihancin sarrafa bayanan da aka riga aka aiwatar kafin ranar janye yardar ba.

Haka kuma, masu bayanai na sirri suna da haƙƙin shigar da ƙorafi ga Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya (NDPC) ko wata hukuma mai kula da wannan fanni, ko kuma su bi duk wata hanyar shari’a da doka ta tanada idan sun yi imanin cewa Mota-Engil Nigeria ba ta sarrafa bayanansu na sirri yadda ya kamata ba, bisa ga tanade-tanaden dokokin da ke aiki da kuma wannan manufar kare bayanai.

Tuntuɓar Mai Kula da Bayanai

Bisa ga dokokin da ke aiki a halin yanzu, Mota-Engil Nigeria ba ta da wajibcin naɗa Jami’in Kare Bayanai (Data Protection Officer – DPO). Duk da haka, domin tabbatar da sadarwa da masu bayanai, an tanadi hanyar tuntuɓa da ke ƙasa domin amsa tambayoyi da bayar da ƙarin bayani kan duk wasu batutuwa da suka shafi sarrafa bayanan sirri da kuma yadda masu bayanai za su iya amfani da haƙƙoƙinsu: privacy@mota-engil.com

Waɗanne Matakan Tsaro Aka Ɗauka?

Mota-Engil Nigeria ta himmatu wajen aiwatar da matakan fasaha da na gudanarwa da suka dace domin kare bayanan sirri daga lalacewa (ko ta hanyar kuskure ko kuma ba bisa ka’ida ba), ɓacewa ta bazata, sauyawa, yaɗawa ko samun damar shiga bayanan ba tare da izini ba. Ana amfani da matakin tsaro da ya dace da haɗurran da ke tattare da sarrafa bayanan, tare da la’akari da yanayin bayanan da ake karewa.

Mota-Engil Nigeria tana gudanar da harkokinta ta hanyar amfani da tsare-tsare da tsarin aiki da aka ƙirƙira domin kare bayanan sirri. Haka kuma, tana aiwatar da hanyoyin gudanarwa da ke hana samun damar shiga bayanan ba tare da izini ba, da kuma hana ɓacewa ko lalacewar bayanan sirri ta hanyar kuskure, tare da bin duk dokoki da ƙa’idojin da suka shafi kare bayanan sirri.

Me yasa zamu iya raba bayanan sirri?

Mota-Engil Nigeria na iya raba bayanan sirri da wasu ɓangarori na uku waɗanda za su iya samun damar amfani da waɗannan bayanai. Waɗannan ɓangarori na uku sun haɗa da hukumomin gwamnati, abokan hulɗa, masu samar da ayyuka da sauran masu ruwa da tsaki. A yayin gudanar da harkokinta, Mota-Engil Nigeria na iya amfani da masu gudanar da ayyuka a madadinta (subcontractors), waɗanda za su sami damar shiga da sarrafa bayanan sirri bisa ga umarnin da muka bayar.

Muna tabbatar da cewa waɗannan masu gudanar da ayyuka a madadinmu suna da isassun matakan fasaha da na gudanarwa domin tabbatar da cewa ana sarrafa bayanan ne bisa ga dokokin kare bayanai da sauran dokokin da suka dace, tare da tabbatar da kare haƙƙoƙin masu bayanai na sirri.

Saboda haka, Mota-Engil Nigeria na iya raba bayanan sirri idan hakan ya zama dole ko ya dace bisa ga dokokin da ke aiki, domin cika wajibai na doka, amsa buƙatun hukumomin gwamnati, idan akwai buƙatar kare muhimman muradun mai bayanan ko na wani ɓangare na uku, domin kare haƙƙoƙi da kadarorin Mota-Engil Nigeria, ko kuma idan an ba da yarda tun da farko domin yin hakan.

A waɗanne yanayi ne zamu iya tura bayanan sirri ka zuwa wasu Ƙasashe?

A yayin gudanar da harkokinta, Mota-Engil Nigeria na iya tura bayanan sirri zuwa wasu ƙasashe na waje – wato ƙasashen da ke wajen Tarayyar Turai (European Union) ko kuma waɗanda ba sa cikin Yankin Tattalin Arzikin Turai (European Economic Area). Ko da yake hakan ba ya faruwa akai-akai, yana iya kasancewa a lokutan da ake kafa hulɗa da wasu ayyuka ko tsarin da Mota-Engil Nigeria ke amfani da su.

A irin waɗannan yanayi, za’a ɗauki duk matakan da suka dace kuma suka zama wajibi domin tabbatar da kariya ga bayanan sirri.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan yanayi shi ne kasancewar Mota-Engil Nigeria a kafafen sada zumunta. A wannan fanni, ikonmu kan yadda waɗannan kafafe ke sarrafa bayanai yana da iyaka (misali wajen gudanar da bayanan mambobi da sauran bayanai na gaba ɗaya). A lokutan da ba mu da ikon sarrafawa kai tsaye, muna ƙoƙarin tabbatar da cewa masu gudanar da waɗannan kafafe suna aiki bisa ƙa’idojin kare sirri da kare bayanai da suka dace. Duk da haka, a lokuta da dama ba mu da ikon tasiri kan yadda suke sarrafa bayanan, kuma ba koyaushe muke da cikakken bayani kan irin bayanan da suke sarrafawa ba.

Masu gudanar da kafafen sada zumunta su ne ke kula da dukkanin tsarin fasahar sadarwa (IT infrastructure) na ayyukansu. Haka kuma, suna aiwatar da nasu manufofi da ƙa’idoji game da kare sirri da kare bayanai, tare da kula da hulɗarsu kai tsaye da masu amfani da kafafensu (musamman waɗanda suka yi rajista a waɗannan kafafe).

Bugu da ƙari, masu gudanar da kafafen sada zumunta ne ke da cikakken alhakin duk wani batu da ya shafi bayanan bayanan martaba (profiles) na masu amfani, waɗanda Mota-Engil Nigeria ba ta da damar shiga ko sarrafawa.

Domin samun ƙarin bayani game da kafafen sada zumunta ke sarrafa bayanai, da fatan za’a duba Manufofin Kare Sirri (Privacy Policies) nasu kamar haka:

Ta yaya muke amfani da “Cookies”?

Domin samun ƙarin bayani game da “Cookies” da kuma yadda Mota-Engil Nigeria ke amfani da su a shafinta na yanar gizo, da fatan za’a duba Manufar Amfani da Cookies (Cookies Policy) ɗinmu.