Titin

Jirgin ƙasa Mai Dorewa Najeriya

Kilomita 400 na layin jirgin ƙasa mai muhimmanci wanda zai haɗa Najeriya da Nijar, zai ƙarfafa zirga-zirgar dama kawo cigaban yankin

Kayan aiki da addadinsu

6,000
2,080
Ayyukan ƙasa 25,000,000
Shinfidar titin Jirgin ƙasan 797,735
Gadoji & Gadar Sama 157
Tashoshi 10
60 UIC kwangirin jirgin 57,000
Kankare 194,155
dutse 840,747

Sansanin Aiki

6

Sashen hada kwalbatoci

3

Sashen hada shimfidar titin

1

Sashen hada kankare

6

Na’urar fasa dutse

3

Manufofi da Alfanu

Manufofin Aikin

Babban manufar Aikin Jirgin ƙasan daya tashi daga Kano zuwa Maradi sune:

  • Inganta Hanyoyin sufuri na iyakoki tsakanin Najeriya da Nijar 
  • Saukaka yawan kashe kudi da kuma taimakawa mutane wurin daukan kayan su cikin aminci da inganci. 
  • Tallafawa yankunan ta fannin kasuwanci, da cigaban tattalin arziki.
  • Samar da hanyar sufuri ta zamani wadda zata rage chunkoson ababen hawa.
  • Tabbatar da bin ka’idojin muhalli, zamantakewa,  lafiya da kuma tsaro.

Amfanin aikin ga Tattalin Arziki da Zamantakewa

Ana sa ran aikin zai samar da manyan fa’idojin tattalin arziki da zamantakewa, ciki har da:

  • Rage farashin sufuri da tsahon lokacin tafiya.
  • Inganta hanyoyin zuwa  kasuwanni na kayan amfanin gona da masana’antu
  • Samar da damar ayyukan yi, kai tsaye ko ta wata hanyar.
  • Zai karfafa tattalin arzikin kananan sana’o’in al’ummar dake kusa da hanyar jirgin kasan.
  • Inganta hanyoyi wajen samun damar hidima da zirga zirgar al’umma.

Amfanin aikin ga Muhalli da Tsaron lafiya

Daga mahangar muhalli da tsaro, aikin zai  bayar da gudummawa kamar haka:

  • Aikin zai rage matsin lamba a hanyoyin mota da kuma rage faruwar  haɗura.
  • Rage hayakin motoci ta hanyar sauya hanyar sufuri daga hanyar motoci zuwa ta jirgin ƙasa.
  • Habbakar ababen more rayuwa na sufuri masu dorewa.
  • Zartarda  da matakan rage illa don kare Nau’o’in halittu daban-daban, albarkatun ruwa, da kuma  al’ummomi  kamar yadda aka tsara a cikin ESIA.

Amfanin aikin ga Hukumomi da Yankuna

A mataki mafi fadi, aikin zai:

  • Ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa tsakanin kasar Najeriya da jamhuniyar Nijar.
  • Tallafawa dabarun cigaban yankuna da tsare-tsaren aiyuka.
  • Shirya  manufofin cigaban duniya da suka shafi sufuri mai dorewa, cigaban da ya hada kowa.

Fasahohin da Aka Yi Amfani da Su

Aikin Jirgin ƙasa na Kano zuwa Maradi yana amfani da fasahohin jirgin kasa na zamani kuma wanda aka tabbatar da ingancinsu, domin samar da aikin gine-gine mai inganci da dorewa bisa ka’idojin kasa da kasa.

Ayyukan gine gine da Tsarin fasaha

Advanced engineering solutions are applied for:

  • Drones (topographic surveys)
  • Bridges, culverts, and drainage structures
  • Earthworks and embankments designed for stability and flood resilience
  • Railway stations, depots, and maintenance facilities

Designs consider local geotechnical and hydrological conditions to ensure durability and climate resilience.
All construction activities follow defined Environmental and Social Management Plans (ESMPs).

Tsarin Makamashi da Ayyukan Amfani

Aikin yana haɗa fasahohin makamashi na haɗe-haɗe, wanda suka haɗa da:

  • Haɗawa zuwa layin wutar lantarki idan yana samuwa. 
  • Injinan dizal masu bada wutar lantarki.
  • Tsarin makamashin hasken rana na photovoltaic a wasu wuraren aikin da sansanin aiki 

Wadannan fasahohi suna rage yawan amfani da mai, hayaki, da kuma kudaden gudanarwa.

Fasahohin tsarin kula da Muhalli

Domin rage illa ga muhalli, aikin yana aiwatar da:

  • Na’urorin masana’antu na kula da Ruwan datti (WWTPs) a sansanin aiki.
  • Rarrabe shara, sake amfani da ita, da kuma tsarin zubar da sharar da aka sarrafa. 
  • Matakan hana zubewar mai da kuma ka’idojin kiyaye afkuwar zubar mai.
  • Fasahohin rage kara da kura.

Tsarin Lafiya, Tsaro, da Kula

Aikin yana amfani da fasahohin kare lafiya da kiyaye haddura, ciki har da:

  • Kulawa zirga-zirga jirgin ƙasa da sauran ababan hawa.
  • Kula da Ka’idojin yanayin muhalli (ingancin iska, ruwa da hayaniyar sauti) 
  • Tsarin shirin kota-kwana na gaggawa.

Tasirin Muhalli, Zamantakewa da Tattalin Arziki

Tasirin aikin ta fannin Muhalli

An tsara Aikin Kano zuwa Maradi don rage illoli ga muhalli. Duk wani yanayi na Rashin dadi ana tafiyar dashi ne ta hanyar aiwatar da tsarin Gudanarwar Muhalli da Zamantakewa (ESMPs), Cigaba da kulawa, hakazalika da tabbatar da maratabar muhalli har zuwa karshen aikin.

Tasirin ta fanni Zamantakewa

Aikin yana tallafawa cigaban yanki ta hanyar samar da ayyukan yi, haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki, da adalci wajen hanyoyin biyan diyya. Ana kula da duk wasu korafe-korafe ta hanyar tsare-tsare, shawarwari da bin matakan da suka dace.

Tasirin aikin ta fanni Tattalin Arziki

Duba da tsarin aikin ta fuskar cigaban kasuwanci, aikin zai hada kan kasar Najeriya da Niger ta fannin samar da aiyukan yi, taimakawa kananan sana’o’i da kuma tallafawa cigaban tattalin arzukin kassa mai dorewa.

Mota-Engil local community support and sustainable development in Nigeria

Manufarmu

Kudurimmu kan Cigaban Kirkire-kirkire da Tasiri ga Al’umma