Dabarun inganta cigaban al’umma
Tsarin da ke haɗa kowa,wajen sauraron al’umma, da samar da fa’ida mai dorewa
Dabarun bunƙasa Al’umma na kamfanin Mota‑Engil Nigeria sun dace da manufofin alhakin zamantakewa (Social responsibility) na rukunin kamfanin, da ƙa’idojin kare ’yancin ɗan Adam, ma’aikata da al’umma, domin tabbatar da cewa kowane aiki yana kawo fa’ida da za’a iya auna shi da kuma mutunta yanayi na musamman na kowane yanki.
Ka’idojin Jagoranci
- Girmama mutuncin ɗan adam da bambancin al’adu.
- Inganta haɗin kan kowa domin cigaba, adalci, da kuma karfafa mu’amala da al’umma.
- Bin dokokin ƙasa da ƙa’idojin ƙasashen duniya.
- Karewa gami da rage mummunan tasiri ta hanyar bada mafita, adalci da haɗin gwiwa.
Tsare-tsare da kuma gudunmawar al’umma
Binciken farko ya haɗa da:
- Ganowa gami da taswirar masu ruwa da tsaki na yankin da kuma rukunin mutane masu bukata ta musamnman.
- Tantance abubuwan da suka shafi al’adu da muhalli masu muhimmanci.
- Kimanta haɗarin zamantakewa da na muhalli.
Tattaunawa da Al’umma
- Tawagar Jami’an Hulda da Al’umma (CLO) masu wakiltar kamfanin ne ke jagorantar wannan.
- Taron bai daya, tambayoyi da amsoshi da kuma tattaunawa ta musamman.
- Sadarwa ta hanyar kafafen yada labarai (rediyo, bayanan wayar da kai ido da ido , da amfani da harsunan gida).
- Rubuce-rubucen martani da kuma tsarin bayar da ra’ayi na hukuma.
Mu’amala ta yau da kullum gami da wakilci mai inganci
- Tattaunawa tare wajen fayyace abubuwan da suka fi muhimmanci.
- Tuntubarsu wajen yanke hukunci.
- Ƙarfafa ƙwarewa da bada horo.
- Kulawa da bibiyar tasiri da cigaban ayyuka bisa jagorancin al’umma.
- Kamfanin Mota‑Engil Nigeria na ɗaukar al’umma a matsayin muhimman abokan hulda, yana kuma tabbatar da cewa dukkan ayyukansa suna kasancewa na bai ɗaya, masu gaskiya da kuma masu mutunta yankunan da suke aiki a cikinsu.
Samar da ayyukan yi ga al’ummar Kasa
Zaburar da ‘yan ƙasa da bunƙasa cigaban da zai haɗa kowa cikin al’umma
Kamfanin Mota‑Engil Nigeria yana sanya ɗaukar ma’aikata ‘yan kasa a dabarunsa Masu dorewa. A dukkan ayyukansa, kamfanin yana ba da fifiko ga ɗaukar ’yan Najeriya domin tabbatar da cewa al’umma na amfana kai tsaye. Tsarin daukar aiki, ingantattun sharuddan aiki da shirye‑shiryen bunkasa ƙwarewa, suna taimakawa wajen haɗa ma’aikata da kuma cigaba na dogon lokaci. Aikin Layin jirgin kasan na Kano–Maradi kaɗai ya samar da dubban ayyukan yi ga al’ummomin yankin.
Manyan Shirye-shirye
- StartME: Shirin horaswa na shekara-shekara ga waɗanda suka kammala jami’o’in Najeriya.
- Horarwar kayyadajjen lokaci: Damar aiki na ɗan gajeren lokaci ga ɗaliban da ke neman ƙwarewar sana’a.
- Shirin yiwa kasa hidima:Damar aiki ga masu yiwa kasa hidima wadanda basu wuce shekaru 30 ba.
- Daukar Ma’aikata ‘yan kasa: Hadin gwiwar al’umma da jami’o’i wajen zakulo mutane masu basira.
- Kamfanin Mota-Engil Nigeria ya himmatu wajen ƙarfafa gina mutane tare da cigaban ƙasa da ƙima mai dorewa ta hanyar ilimi, damarmaki, da haɗa kowa cikin cigaba.
Ayyukan Al’umma
Haɗa kowa wajen cigaba, kusanci da al’umma, da tsarin zamantakewa da ake iya aunawa.
Aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Maradi ya ƙunshi tsari mai kyau na alhakin zamantakewa, maida hankali kan cigaban kowa da kowa, kusanci da al’umma da kuma ƙimar zamantakewa ta gaske a dukkanin inda titin ya bi.
Hulɗa da Al’umma gami da Tattaunawa
- Taron al’umma da dandalin tattaunawa.
- Zauren tattaunawa da ke mai da hankali ga mata, makiyaya, da manoma.
- Kwamitocin canja matsugunin jama’a da kula da korafe-korafe a matakin ƙaramar hukuma, jiha, da ƙasa.
Waɗannan hanyoyin suna tabbatar da gaskiya, shigar al’umma cikin harkokin aikin, da kuma amsa bukatun al’umma yadda ya kamata.
Tallafi kai tsaye ga al’umma
- Ba da gudummawar kujerun makaranta da aka ƙera daga katako da akayi amfani da shi.
- Samar da murafan magudanai na siminti domin shimfiɗa hanya ga asibitoci da wuraren jama’a.
- Kayan gini don inganta hanyoyin mota da rage haɗarin ambaliya.
- Tallafawa da Kayan aiki don samar da kayan adon daki.
- Tallafawa wajen gina hanyoyin tsallakawa ga masu tafiya a ƙafa domin kiyaye hadura kusa da makarantu.
Wayar da kai akan Lafiya da Muhalli
- gangamin wayar da kai kan muhalli
- Wayar da kai don kiyaye hadura akan titin jirgin ƙasa
- Ranakun tsaftace muhalli na al’ummar gari da ma’aikata
Tallafi ga masu bukata ta musamman
- Raba murhunan tukwane masu amfani da makamashi mai inganci.
- Samar da kananan kujerun zama domin inganta jin daɗi.
Samur da ruwa hadi da tasirin sauyin yanayi
- Rijiyar burtsatse wadda ke samar da ruwa ga kauyukan da ke kusa. Sake amfani da gurbataccen ruwan da aka tace daga injinan kula da gurbataccen ruwa, domin rage kura da kuma ban ruwa.